(ABNA24.com) Wakilan bangarorin dake rikici a kasar Libiya, sun cimma matsaya a Geneva kan wani kudirin da ya jibanci tsagaita bude wuta a kasar dake fama da rikici.
Kudirin kuma zai baiwa MDD, damar sanya ido kan shirin komawar fararen hula a yankunansu a cewar MDD.
Nan gaba ne wakilan bangarorin dake rikici a kasar da suka halarci taron tattaunawar na Geneva, zasu gabatar da kudirin ga jagororinsu domin dubawa, a wani mataki na share fagen wani taro a watan gobe domin sake komawa kan teburin tattaunawa domin shawo kan rikicin kasar, kamar yadda tawagar wanzar da zaman lafiya ta MDD, a Libiya (Manul) ta sanar a yau.
A makon da ya shude ne tawagar gwamnatin kasar ta Libiya dake samun goyan MDD, ta Fayez Al-sarraj da kuma bangaren Khalifa Haftar dake da rike da ikon gabashin kasar suka koma bakin tattaunawa a Geneva a shiga tsakanin MDD.
/129